Bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumunta inda aka ga wani dansandan Najeriya a babban birnin tarayya, Abuja yana tangadi.
Wanda suke wajan dai sun yi amannar cewa giyace yasha da rana tsaka inda aka ji wata murya a cikin Bidiyon na kiran sunan dansandan da Garba Salisu.
Rahoton ya bayyana cewa an kwace Bindigar dansandan dan kada yayi aika-aika.
