Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike tare da Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da magoya bayansu sun rufta cikin wani dandamalin tsayuwa a wajan taron zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na PDP da aka yi jiya da dare.
Saidai da alamu babu wanda ya jikkata sosai, dan duk sun wuce daga wajan.
Atiku Abubakar ne dai ya lashe wannan zabe da tazarar kuri’u sama da 100.