Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Aminu Ibrahim Daurarawa ya bayyana yanda suka samu wani labari mara dadi tsakanin wasu ma’aurata.
Malam ya bayyana a wani wa’azi da yayi cewa, wata matace mijinta ya kamata tana soyayya da mazaje daban-daban a shafukan sada zumunta.
Bayan da ya kamata, sai ta amince ta yi laifi ta bashi hakuri kuma aka ci gaba da zama, saidai daga baya an bashi shawarar ya sayi layin da bata sani ba ya mata magana dan tabbatar da ta daina.
Ya kuwa aikata hakan kuma sai ta ci gaba inda taita zagin mijin mata da fadar halayensa marasa kyau.
Ya gaya mata cewa da zata yadda mijinta ya saketa, zai aureta, nan kuwa tace ta amince, ta je ta fara yiwa mijinta balbalin bala’i cewa sai ya saketa.
Dan jin cikakken labarin danna nan ku kalli bidiyon