Majalisar Kasar Ingila ta yi zama akan bukatar sakawa Najeriya takunkumi saboda zargin harbe-harben da aka yi a Lekki Toll Gate yayin zanga-zangar SARS.
Gwamnatin tarayya ta karyata cewa an rasa rayuka a wajan inda tace Bidiyon karyane kawai aka rika yadawa a shafukan sada Zumunta.
Wani dan majalisar kasar ta Ingila ya bayyana bukatar cewa ya kamata a dakatar da masu satar kudin Najeriya suna kaiwa kasar ta Ingila suna boyewa.
A wani Bidiyo da ya watsu sosai a shafukan sada zumunta, an ji dan majalisar na bada Misali da yanda tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon ya kwashi rabin kudin babban bankin Najeriya, CBN ya tafi dasu kasar ta Ingila.
How am I just hearing this for the first time?! 😳😂.
A UK Parliament member just revealed that General Gowon, during his time, carted away with HALF OF CBN!! Bruh, HALF OF CBN 😂?!!! pic.twitter.com/cygw5XOGlh— Niklaus 🥺 (@LifeOfChika) November 23, 2020