Bidiyon wata mata da ta yi ikirarin cewa ita shaida ce a rikicin Kabilanci da ya barke a Shasha dake Akinyele jihar Oyo ya watsu sosai.
Ta yi ikirarin cewa ba Bahaushene ya tada rikicin ba. Tace wani dan kasar Nijar ne ya zubar da Tumatur a gaban shagon wata Bayerabiya.
Sai Bayerabiyar tace sai ya kwashe ya kuma wanke mata gaban shago, Shine yace shi bai san inda zai samo Ruwan da zai wanke mata ba. A nan ne wani Bayerabe ya ashiga maganar inda har takaiga ya mari Dan kasar Nijar din, tace shine dan kasar Nijar din ya rama. Ta kara da cewa bayan marin shine Bayeraben ya fadi kasa.
An garzaya dashi Asibiti, Inda acan Likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu. Tace shine wani ya wallafa a kafar sada zumunta, aka fara kashe-kashe.
https://twitter.com/Abdul_A_Bello/status/1361249613387345922?s=19