Sanadiyyar ruwan wutar da sojojin Najeriya kewa ‘yan Bindigar Zamfara, sun canja Maboya inda suka koma tsakanin wasu tsaunuka a dajin Doumbourou.
Sojojin sun samu wadannan bayanai inda suka tashi jirgin sama dan tabbatarwa. Daga baya an aika jirgin yaki da yayi wa sabuwar mabiyar ‘yan Bindigar ruwan bama-bamai.
OPERATION HADARIN DAJI: AIR COMPONENT TAKES OUT ARMED BANDITS’ CAMP, ELIMINATES SEVERAL FIGHTERS AT DOUMBOUROU FOREST IN ZAMFARA STATEhttps://t.co/QrZKlWbWco pic.twitter.com/gM8uyfcIST
— DEFENCE HQ NIGERIA (@DefenceInfoNG) July 25, 2020
Wasu dake shirin tserewa suma sun gamu da fushin sojojin inda suka rika musu luguden wuta, kamar yanda za’a iya gani a wannan bidiyon.