Wednesday, June 3
Shadow

Bidiyo:Yanda Sojojin Saman Najeriya suka yi Luguden Bama-bamai akan ‘yan ta’addar Katsina da zamfara suka kashe 135

Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa sojojin sama dake rundunar Operation Hadarin daji ta yi kaca-kaca da maboyar wasu ‘yan ta’adda a jihohin katsina da Zamfara.

 

Harin ya farune tsakanin Ranekun 20 zuwa 22 ga watan Mayu inda aka kai shi kan kauyukan Danya dake karanar hukumar Jibia, da Dan Musa dake karamar hukumar Katsina.

 

An kuma kaiwa maboyar ‘yan ta’addar dake Maikomi a Birnin Magaji da kuma Karamar Hukumar Zurmi dake Jihar Zamfara.

 

Harin yayi Sanadin lalata maboyar Barayin Shanun inda aka kashe 135 wasu kuma da dama suka tsere da raunukan Bindiga

A jiya ne dai muka mawo muku yanda Hukumar sojin Sama ta aika karin yawan dakaru Katsina dan maganin ‘yan Bindigar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *