Ma’aikatar kula da ibtila’i da jinkai ta bayyana cewa, gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari na kashe Biliyan 12 a duk wata wajan ciyar da dalibai abinci.
Jami’in hukumar, Umar Bindir ne ya bayyana haka a wajan wani taro da aka gudanar a Abuja.
Ya bayyana cewa, ciyar da daliban na da matukar tsada, yace dalibai Miliyan 10 ne ake ciyaswa a fadin Najeriya akan Naira 100 kan kowane dalibi.
Yace bayar da abincin na matukar jawo hankalin dalibai zuwa makaranta.