fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Bindugu muka sayo da kudin fansa naira miliyan 60 da gwamnatin Najeriya ta bamu, cewar shugaban ‘yan bindiga na Zamfara

Kasurgumin dan bindigar da yayi garkuwa da dalibai kusan 300 a makarantar mata ta gwamnati ya bayyana cewa naira miliyan 60 gwamnati ta basu kudin fansa.

‘Yan bindigar sunyi garkuwa da matan ne a shekarar 2021 dake Jangebe a karamar hukumar Talata Marafa a jihar Zamfara.

Kuma ya bayyanawa manema labarai na BBC African Eye cewa sunyi amfani da makudan kudin da gwamnatin ta basu ne sun sayo makamai domin su cigaba da ta’addancin nasu.

Tuni ‘yan bindigar suka sako daliban bayan wasu ‘yan kwanaki da sukayi a hannunsu saboda gwamantin jihar Zamfara ta biya masu bukatunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.