Birnin Birmingham wanda shine na biyu mafi girma a kasar Ingila yace ya talauce bashi da kudi.
Birnin ya kasa biyan Albashin ma’aikata na mafi karancin Albashi wanda jimullarsa ta kai dala Miliyan $956.
Dalilin haka, Birnin ya bayyana cewa ya dakatar da duk wasu ayyuka a cikinsa in banda masu matukar Muhimmanci, kamar su Asibiti, tsaro da sauransu.
Birnin dai ya zargi cewa, dakatar da basu fan Biliyan £1 da gwamnatin tarayyar kasar ta yi ya taimaka wajan jefasu cikin wannan ibtila’i.