fbpx
Monday, March 1
Shadow

Biyan kudin fansa ba shine mafita ba, a samarwa makarantun ‘ya’yan Talakawa tsaro kamar yanda ake samarwa na masu kudi>>Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da satar daliban sa aka yi a Kagara, Jihar Naija.

 

Atiku ya bayyana cewa matsalar tsaron Najeriya ta kai wani hali mafi muni wamda ya kamata ace an dauki matakin magance matsalar.

 

Atiku yace yanzu ba lokacin dorawa wani laifi bane, yace kamata yayi a rika daukar matakan hana faruwar irin wannan abu, ba sai ya faru ba azo anata neman yanda za’a maganceshi.

 

Yace kamata yayi gwamnatin tarayya ta samar da tsaro a irin wadannan makarantu idan kuma ba zata iya ba, ta baiwa gwamnatocin jihohi damar yi. Yace ya kamata kamar yanda makarantun ‘ya’yan Masu Kudi ke samun Tsaro suma ‘ya’yan Talakawa a asama musu.

“As a nation, we must be willing to provide the same level of security that we provide for the schools that the children of the elite attend, for schools that the children of other classes of Nigerians attend.

“I pray that the Kagara staff and students are rescued, and for peace to return to Nigeria.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *