fbpx
Monday, June 27
Shadow

Biyu babu: Dan takarar daya yi nasarar samun tikitin sanatan Arewacin Yobe yace ba zai janyewa Ahmad Lawal ba

Dan takarar daya yi nasarar samun tikitin kujerar sanata na arewacin jihar Yobe, Bashir Sheriff Machina yace ba zai janyewa shugaban sanatoci ba, watau Ahmad Lawal.

Machina ya bayyana cewa mutane da dama sun kira shi sun bukaci cewa ya janyewa shugaban sanatocin amma ya turawa shugaban APC sako cewa ba zai janye masa ba.

Sanata Ahmad Lawal ya fadi zaben fidda gwani na APC kuma gshi yayi asarar kujerarsa ta sanatan arewacin Yobe wadda ya kasance akai na tsawon shekaru 15.

Leave a Reply

Your email address will not be published.