Wednesday, December 4
Shadow

Blinken a Masar don inganta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Masar domin samun goyon bayan yankin ga yarjejeniyar zaman lafiyar Gaza da shugaba Joe Biden ya gabatar kwanan nan.

Wannan ziyarar dai ita ce ziyara ta takwas da Blinken ya kai yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan ɓarkewar rikicin Gaza.

Blinken zai gana da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi kafin ya tattauna da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a yau Litinin.

Masu shiga tsakani a yankin ciki har da Qatar, sun shafe watanni da dama suna ƙoƙarin sasantawa tsakanin Isra’ila da Hamas.

Netanyahu ya ci gaba da jajircewa wajen ƙin amincewa da duk wani tsagaita bude wuta har sai an wargaza sojojin Hamas da kuma sako duk waɗanda aka yi garkuwa da su.

Karanta Wannan  Ina baiwa gwamnati Shawarar ta cire tallafin man fetur gaba daya>>Dangote

A karshen makon da ya gabata, sojojin Isra’ila sun kuɓutar da wasu mutane huɗu da Hamas tayi garkuwa da su bayan kazamin fada da Hamasɗin a ciki da wajen sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat.

A cewar ma’aikatar kiwon lafiya ta Hamas a Gaza, harin ya yi sanadin mutuwar mutane 274 da suka hada da kananan yara da wasu fararen hula, yayin da Isra’ila ta sanar da mutanen da suka jikkata akalla su100.

Bayan kai farmakin, shugaban siyasar Hamas ya bayyana cewa, ƙungiyar ba za ta amince da tsagaita bude wuta ba, sai dai idan ta samar da tsaro ga Falasdinawa.

Blinken na da burin yin amfani da ziyarar tasa domin shawo kan shugabannin Larabawa da su matsa wa Hamas lamba ta amince da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da sako mutanen da akayi garkuwa da su da Amurka ke matsawa.

Karanta Wannan  Tauraruwar Fina-finan Hausa,Asma Wakili ta ajiye mukamin da Gwamnan Kano,Abba Gida-Gida ya bata ta fice daga jam'iyyar NNPP zuwa APC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *