Wani boka a kasar Ghana ya kira ‘yansanda suka kama wani mahaifi da ya kai masa ‘ya’yansa 2 ya mai tsafin kudi.
Mahaifin ya dauki diyarsa daga makaranta ya wuce da ita wajan bokan. To saidai ga alama shima bokan abin yafi karfinsa shiyasa ya kira ‘yansanda.
Bokan yace mutumin ya kuma gaya masa zai sadaukar da ‘ya’yansa biyu wajan yin tsafin idan dai zai samu kudi.