fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Boko Haram na da karfi sosai a wasu ƙananan hukumomin Borno>>Ndume

Sanata mai wakiltar yankin kudancin jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya ya tabbatar wa BBC batun da Gwamna Zulum ya ambata cewa akwai wasu ƙananan hukumomin jihar da ƴan Boko Haram ke da ƙarfi a can.

Sanatan ya faɗi hakan ne a wata hira a ranar Alhamis, sakamakon rahotannin da aka ambato Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar na cewa har yanzu ƙananan hukumomin Abadam da Guzalama na ƙarƙashin ikon Boko Haram.

Ya ƙara da cewa amma fa Boko Haram ɗin yaƙin sari ka noƙe suke yi. Ba za ka ce ga ƙaramar hukuma taƙamaimai da ke hannunsu ba amma sukan yi gayya ne su je su kai hari.

Wannan lamari da ke faruwa a ƙananan hukumomin Abadam da Guzalama da wasu mazauna yankin suka ce rashin tabbacin tsaron da ya sa har yanzu kungiyar Boko Haram ɗin ke cin karenta babu babbaka a wasu yankunan jihar ya yi sanadin jingene batun mayar da ƴan gudun hijira garuruwansu.

Gwamnatin jihar Bornon a yanzu haka tana ta aiki kan shirin mayar da ‘yan gudun hijira ƙananan hukumominsu na ainihi, sai dai ana fuskantar tangarɗa nan da can game da lamurran tsaro a wasu wuraren.

Wani mazaunin karamar hukumar Abadam da yanzu haka yake gudun hijira a birnin Maiduguri ya shaida wa BBC cewa a yanzu haka duk jama’ar garin Abadam sun tsere.

“Wasu suna Damaturu wasu kuma suna garin Wanzam da Diffa da sauran wurare, yanzu haka cikin Abadam dai babu mutane.

“Sai dai duk da cewa akwai jami’an tsaro a wajen sosai amma hakan ba ya hana ƴan Boko Haram kai hari jefi-jefi,” a cewar mutumin.

Sanata Ndume ya ƙara da cewa: “Ko a ta wajenmu a kudancin Borno akwai ƙananan hukumomi guda kusan wanda ɓangaren ƙungiyar ISWAP ke yaɗuwa a wajen kuma suna mana ɓarna.

“Su ne ma suka kashe mana wani babban janar ɗin nan a kwanaki a kusan ƙarshen shekarar 2021.

“Muna kuma samun labarin cewa suna tare hanya tsakanin Dambua da Biu inda suke karɓar kuɗaɗe a hannun matafiya da mutanen ƙauyukan da suke wajen.

“Sannan har yanzu mun san cewa akwai ƴan Boko Haram a Dutsen Gwoza daga ɓangaren Najeriya wato a Tsaunukan Mandara ta wajen ƙaramar hukumata ta Gwoza.

“To amma jami’an tsaro sun ba mu tabbaci a kan cewa suna sane da haka kuma suna aiki don yin wani abu akai,” in ji shi.

Sanata Ndume ya ƙara da cewa akwai ƙauyukan da mutane suka tsere daga cikinsu da ba a san halin da ake ciki ba a yanzu, kuma babu wanda ya san ko wa yake riƙe da su ko masu zama a wajen.

“Kamar yanzu a ƙaramar hukumar Damboa akwai mutane da dama da suka tsere da wasu ƙauyukansu a yankin.”

An shafe shekara 10 ana fama da rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya haddasa yawaitar ƴn gudun hijira a faɗin jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.