fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Boko Haram na daukar kananan ‘ya’yanmu aiki>>Gwamna Zulum ya koka

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya koka da cewa Kungiyar Boko Haram na daukar kananan yara dake sansanonin Gudun Hijira daban-daban aiki.

 

Ya bayyana hakane a yayin ganawa da wasu ‘yan Majalisa da suka kai mai ziyara Ofishinsa dake Maiduguri.

Gwamnan yace akwai babbar matsala wadda za’a iya shiga wadda tafi wadda ake ciki yanzu muddin ba’a yi kokarin mayar da wanda suke sansanonin ‘yan Gudun hijira gidajen su ba.

 

Gwamnan yace akwai sama da mutane Miliyan 1 dake zaune a sansanonin gudun hijirar kuma Boko Haram na daukar ‘ya’yanmu kanana aiki saboda rashin aikin yi.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Rundunar soji ta damke 'yan bindigar da suka kashe mutane 40 a cocin katolika ta jihar Ondo

 

Gwamnan yace maslaha daya ke da akwai shine a samu a mayar da mutane gidajen su su ci gana da harkar noma da sauran sana’o’i da suka saba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.