Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce mayakan Boko Haram na da almajirai a matsayin mambobin su daga Arewa.
Ganduje, wanda ya yi magana a lokacin kaddamar da littafin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a ranar Talata a Abuja, ya bayyana batun Almajiri a matsayin babbar matsala ga Arewa.

“Babu shakka kungiyar Boko Haram ta yi nasara a Najeriya saboda suna da tushe da cibiyar daukar ma’aikata a cikin Almajirai wadanda ba su da zurfin tunani,” in ji Ganduje.
Gwamnan ya yaba wa tsohon Shugaban kasar kan gudummawar da ya bayar wajen inganta darajar ilimi a kasar nan, musamman ma, kafa makarantun Almajiri a lokacin mulkinsa.
“Jonathan ya fadada kuma ya zurfafa tsarin Almajiri kuma muna gyara tsarin Almajiri a Kano kuma muna samar da karin irin wadannan makarantu a jihar.
“Tsarin Almajiri ya kasance mai kyau lokacin da aka kirkireshi saboda ya taimakawa yara karatun Alkur’ani mai girma.
“Babu batun bara a lokacin.
“Amma daga baya, tsarin ya kasance cikin lalata, shi yasa muka tsinci kanmu a wannan halin da muke ciki.
“Tsarin karatun a lokacin kawai karatun Alkur’ani ne mai girma, amma hakan bai isa ba ga ilimin addinin Musulunci,” in ji Ganduje.
Da yake magana, Jonathan ya ce: “Muna bukatar daukaka darajar Almajiri daga matsayin da suke a yanzu.
“Idan muka barsu yadda suke, hakan zai haifar mana da matsaloli masu yawa.”
Masu martaba a wajen taron sune; Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel; Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar; Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed wanda ya samu wakilcin tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Tanimu Turaki, da sauransu.