Rahotanni sun bayyana cewa, Kungiyar ISWAP data balle daga Boko Haram sun fara kai hare-hare jihohin Yarbawa.
Hari na baya-bayannan da aka kai wata coci dake Owo a jihar Ondo da ya kashe mutane da dama ya tayar da hankalin mutane.
Saidai gwamnatin tarayya tace kungiyar ISWAP ce ta kai harin.
Mutane akalla 40 ne aka ruwaito sun mutu sanadiyyar wannan hari.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka a ganawarsa da namema labarai ranar Alhamis.
Yace tuni jami’an tsaro sun fara bin sahun wanda suka yi wannan aika-aika.