fbpx
Saturday, February 27
Shadow

Boko Haram Sun Kaiwa Tawagar Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff Mummunan Hari

INNALILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI’UN

Dazun nan Boko Haram suka kaddamar da mummunan harin ta’addanci akan tawagar tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff lokacin da suke rakiyar tawagar tsohon gwamnan daga Abuja zuwa garin Maiduguri don yin jana’izar mahaifinsa da ya rasu, sai Boko Haram suka kaddamar musu da mummunan hari a daidai garin Auno dake kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

 

 

‘Yan ta’addan sun hallaka wasu jami’an ‘yan sanda masu bada kariya na musamman Special Protection Unit (SPU) rundina ta 12 kuma harin ya rutsa da fararen hula, gawarwakinsu yana asibitin kwararru na garin Maiduguri.

 

 

Wadanda suka samu shahada Insha Allah a wannan mummunan hari sune Cpl Mustapha Yunusa, Cpl Abubakar Idris, sannan ‘yan ta’addan sun tafi da bindigogin jami’an, wasu ‘yan sandan kuma har yanzu ba a gano inda suke ba.

 

 

Sai dai wannan harin bai rutsa da tsohon gwamnan ba, saboda jirgin sama ya hau daga Abuja zuwa Maiduguri abinsa.

 

 

Muna rokon Allah Ya karbi shahadar wadannan jaruman ‘yan sanda, Allah Ya kawo mana karshen ta’addancin Boko Haram da masu tallafa musu. Amin.

Daga Datti Assalafiy

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *