Ranar Alhamis an samu sabbin Rahotannin dake cewa, Kungiyar Boko Haram ta kashe mutane 23 a Arewa maso gabashin Najeriya.
Tun ranar Talata ne Boko Haram ta kai harin amma ba’a samu bayanai ba sai ranar Alhamis saboda ta lalata na’urorin sadarwar yankin.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya, AFP yace zuwa yanzu an ga gawarwakin mutane 23 da harin ya rutsa dasu.
Mutane 3 sun kubuta amma akwai wasu 24 da ba’a san inda suke ba.
Wani shaida ya bayyana cewa, akwai yiyuwar Boko Haram ta yi garkuwa da sauran mutanen ne.