fbpx
Monday, March 1
Shadow

Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya 7 da ‘yansanda 4

A jiyane dai hutudole ya kawo muku Rahoton cewa, Boko Haram sun kai hari garin Baymari na jihar Yobe.

 

A sabon Rahoton BBChausa, Boko Haram din sun kashe Mutane 10 da kuma ‘yansanda 4.

 

Rahotanni daga jihar Yobe a yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayaƙan Boko Haram sun kai hari ƙauyen Bayamari inda suka kashe ƴan sanda da wasu mutanen gari.

Wani mazauni yankin ya shaida wa BBC cewa ƴan sanda huɗu maharan suka kashe da mutanen ƙauyen kusan mutum 10.

Bayamari na cikin ƙaramar hukumar Dapchi ne inda Boko Haram ta taɓa sace ƴan mata ɗaliban makarantar sakandare.

Kuma wasu bayanai sun ce an kashe ƴan sandan ne a yayin da suke ƙoƙarin kare mutanen ƙauyen daga ƴan ta’addan.

A wani Sabon Rahoto kuma, Boko Haram sin sun kaiwa Sojojin Najeriya Harin Kwantan Bauna da yayi sanadiyyar mutuwar sojojin 7.

Sojojin da aka kashe suna rundunar 153 Battalion ne dake Marte kuma harin ya je musu a bazata ranar 15 ga watan Fabrairu.

Lamarin ya farune da misalin karge 10 na safe, Sojojin sun yi kokarin tsayawa dan kare sansanin nasu amma Boko Haram sin suka ci karfinsi, Kamar yanda Premium times ta ruwaito.

It was gathered that they put up a strong fight to defend their base and ward off the insurgents, but were overwhelmed “because they could not withstand the superior firepower of the terrorists”.

Military insiders reportedly said Monday’s attack on Marte Local Government by the extremist Boko Haram group makes it the third onslaught in the area in a month.

 

The terrorists had ambushed soldiers at the location on January 10 and 15. The casualty rates from those attacks are unknown.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *