fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Boko Haram sun koma garkuwa da mutane>>Sarkin Musulmi

Me Alfarma Sarkin Musulmi,  Alhaji Sa’ad Abubakar na III ya bayyana cewa Boko Haram sun koma yin Garkuwa da mutane dan neman kudin fansa.

 

Ya kuma yi Allah wadai da harin satar daliban Makarantar Kagara da aka yi a Jihar Naija.

 

A sanarwar Sakataren JNI, Dr. Khalid Abubakar Aliyu ya fitar, ya bayyana cewa sace daliban abin takaici ne wanda yasa dole a yi tambayar inda jami’an tsaro dake aikin samar da bayanan Sirri har haka ta faru?

 

Yace bai kamata ace an bar lamarin ya faruba inda yace ba’a koyi darasi daga irin hakan data faru a Dapchi, Kankara, da Chibok ba. Ya bayyana cewa wannan salo ne na Boko Haram dan ganin an daina Karatun Boko.

 

Ya jawo hankalin Gwamnati data tashi tsaye wajan maganin lamarin.

 

“The Sultan of Sokoto is in utter disbelief and astonishment that students could be abducted from school, despite the not too long ago Kankara episode, just a few days after the kidnap of passengers on board the Niger State Transport Authority (NSTA) bus in the same Niger State.

“This is absolutely incredible, despicable and condemnable. Ordinarily, the school abduction should have been averted if there were adequate security surveillance and alertness around our boarding schools. These unfortunate trends are becoming the new normal.

 

“Worst still, Kagara town and by extension Niger State, has become infamous, given the serial attacks by bandits and other criminals in recent past.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *