Rahotanni daga garin Kukawa na jihar Borno na cewa mayakan Kungiyar ISWAP data balle daga kungiyar Boko Haram sun dirarwa garin da yammacin jiya, Talata.
Lamarin ya farune jim kadan bayan da mutanen garin da suka shafe shekaru 2 a sansanin gudun hira suka koma garuruwansu. Hutudole ya tattaro muku daga rahoton kamfanin dillancin labaran AFP yanda wani shugaban ‘yan Vigilante, Babakura Kolo ya tabbatar da faruwar lamarin.
Zuwa yandai babu wata sanarwa daga hukumar soji kan harin.