fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Boko Haram sun sake kai hare-hare da safiyar Yau Asabar a kananan hukumomi 2 na jihar Borno

Mutanen da ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne a yanzu haka, sukai hari kan wasu kananan hukumomi biyu na jihar Borno a lokaci guda, in ji majiyoyin tsaro.

An samu labarin cewa, maharan sun mamaye garin Monguno da misalin karfe 11:30 daidai, suna harbi a kokarin su kwace garin.
A cewar majiyar tsaro har yanzu anajin harbe-harben  bindiga tsakanin sojoji da ‘yan ta’addan.
Ma’aikatan wata kungiyar sakai ta INGO sun shaida wa manema labarai cewa ana jin karar harbin bindiga a ko’ina.
“Ayanzu haka da nake magana da kai, garin Monguno na cikin hari da yan kungiyar Boko Haram suka kawo, ana jin karan fashewar abubuwa, sojojin na kokarin mayar da harin. Muna cikin wani hali, don Allah a yi mana addu’a. “
Kazalika, maharan sun kai hari kan wani kauye mai suka Usmanati Goni, karmar hukumar Nganzai a safiyar ranar Asabar.
A cewar wata mafarautan yankin, maharan sun zo ne da misalin karfe 10 na safe, suna ruwan harsasai kan farar hula.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  'Yan ta'addan ISWAP sun kai sabon hari a Maiduguri sun kashe dan samda guda

Leave a Reply

Your email address will not be published.