Rahotanni sun bayyana cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya shirya tsaf dan bayyana wanda zai masa mataimakin shugaban kasa nan da ranar Laraba.
Rahoton yace daga Arewa maso gabas ne Tinububzai dauko wanda zai masa mataimakin.
Punchng da ta kawo rahoton tace Tinubu zai kammala ganawa da gwamnoni da wakilan jam’iyyar tasa kamin daga baya ya bayyana abokin takararsa.
Akwai dai yiyuwar musulmi ne Tinubu zai dauka a matsayin mataimakin nasa.