fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Borussia Dortmund 1-0 Hertha Berlin: Emre Can ya taimakawa Dortmund a wasan da suka buga jiya

Borussia Dortmund sun cigaba da fafatawa domin suga sun kerewa abokan hamayyar su wato Bayern Munich wanda sune a saman teburin gasar Bundlesliga a yanzu yayin da suka wuce Dortmund da maki bakwai.

A jiya Dortmund suka buga wasa tsakanin su da Hertha Berlin kuma sun yi nasarar jefa kwallo guda a wasan, yayin su kuma abokan hamayyar su Munich suka yi nasarar tashi a 4-2 tsakanin su da Leverkusen duk dai a jiyan.
Dortmund sun barar da kwallaye dama yayin da tauraron Ingila Jadon Sancho shima ya barar da kwallaye biyu masu kyau, daga bisani kuma Emre Can yayi nasarar cin kwallon daya bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Yayin da aka kusa gama wasan, gabadaya yan wasan Dortmund dana Hertha Berlin guda 22 sun tsugunna a tsakiyar filin wasan sun yi zanga zangar mutuwar wani bakin fata a kasar Amrika George Floyd wanda ya mutu ranar 25 ga watan mayu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Zan iya rantsuwa da alkur'ani cewa Atiku ne ya lashe zaben shekarar 2019, cewar Buba Galadimar

Leave a Reply

Your email address will not be published.