fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

BUA Ya Bada Motocin Daukan Mararsa Lafiya 3, Da Naira Miliyan 200 Ga Gwamnatin Jihar Adamawa

Gwamna Ahmadu Fintiri ya samu kyautar Naira miliyan 200 da motocin daukar marasa lafiya guda uku daga kamfanin BUA a matsayin tallafi a yakin da ake yi da annobar coronavirus a jihar Adamawa.
Alhaji Abdulsamad Rabiu, wanda tsohon Ministan Lafiya na Kasar, Dakta Idi Hong ya wakilta, ya ce wannan matakin zai taimaka wa jihar don dakile yaduwar cutar ta corona.
Dakta Hong ya ce ya zuwa yanzu, kungiyar ta BUA Group Foundation ta kashe kusan Naira biliyan 7 don taimakawa gwamnatoci da kungiyoyin kamfanoni a duk fadin kasar sannan ya jaddada cewa kamfanin zai ci gaba da ba da taimako ga ci gaban bil’adama.
Da yake mayar da martani bayan da ya karbo takardun motocin da kuma cek din na Naira miliyan 200, Gwamna Umaru Fintiri ya nuna godiyarsa ga Shugaban kungiyar ta BUA saboda tallafin a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ke cikin mawuyacin hali.
Gwamnan ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta yi amfani da motocin da kudin da aka bayar don abin da aka yi niyya, tare da bayyana cewa an riga an adana Naira miliyan 200 a asusun ajiya na coronavirus na jihar.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati tana karbar gudummawar ne daga hannun ‘yan kasa a cikin jihar tun bayan barkewar cutar corona a cikin Adamawa tare da yin kira ga sauran kungiyoyin agaji da suyi koyi da kwazon kungiyar BUA don taimakawa gwamnatoci don yakar cutar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Wannan take hakkin bil'adama ne>>Fasto dan luwadi yayi Allah wadai da hukuncin kisan da aka yankewa 'yan Luwadi a Bauchi

Leave a Reply

Your email address will not be published.