A matsayin wani bangare na gudummawar da take bayarwa ga cigaban al’ummomin da suka karbi bakuncin ta, kamfanin simintin BUA, daya daga cikin manyan kamfanonin siminti a Afirka ya bayar da gudummawar taransifomomi 6 na 500KVA domin bunkasa samar da wutar lantarki ga al’ummomin Okpella na jihar Edo.

Haka kuma, kamfanin ya sanar da bayar da tallafin karatun mutane 100 ‘yan asalin Okpella tare da samar da motocin sintiri na tsaro ga jami’an tsaro a cikin al’umma.
Da yake jawabi game da gudummawar, Injiniya Yusuf Binji, Manajan Darakta kuma Shugaba na kamfanin simintin BUA, ya ce alhakin kamfanin simintin BUA na zamantakewar jama’a wani bangare ne mai muhimmanci na kamfanin kuma sakamakon haka, ya himmatu ga ci gaban al’ummomin da ke karbar bakuncin aiki shi.
Game da motocin jami’an tsaro, Binji ya lura cewa wannan zai taimaka wajen bunkasa karfin hukumomin tsaro a cikin al’umma don samar da kyakkyawan tsaro ga mazauna da kasuwancin Okpella.