Kamfanin BUA ya bayyana cewa zai gina Kamfanin sumuti a jihar Adamawa. Hakan ya fito daga bakin shugaban kamfanin, Abdulsamad Rabiu yayin da suka kaiwa gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri ziyarar bang girma.
Abdulsamad yace sun gano akwai albarkatun siminti a kananan hukumomin Guyuk da Lamurde kuma suna shirin kafa kamfani a kananan hukumomin sannan kuma zasu samar da wutar lantarki wadda zata baiwa kamfanin wuta ta kuma baiwa kananan hukumomin 2 suma wutar.
Yace kamfanin zai samar da ayyukan kai tsaye da wanda bana kai tsaye ba har Dubu 8. Yace sun yi wannan yunkurine a kokarinsu na ci gaba da samar da amfani da abubuwan da aka sarrafa a cikin gida Najeriya sannan kuma suna bukatar goyon baya gwamnatin jihar.
A nashi bangaren, Gwamna Fintiri ya bayyana cewa, yayi matukar farin ciki kuma yana maraba da wannan aniya inda yace wannan na kan hanyar kokarin da gwamnatinsa take na samar da kayan amfani na cikin kasa.
Ya kara da cewa idan aka samar da kamfanin, ita kuma gwamnati zata bayar da tsaro.