fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Buhari bai ga bidiyon da ‘yan Bindiga suka ce zasu saceshi ba, ni naje na gaya masa, kuma ya gayamin matakin da ya dauka>>Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, shine ya je ya gayawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa, ‘yan Bindiga na barazanar saceshi.

 

Yace a lokacin da ya gayawa shugaban kasar, bai ga bidiyon ba, yace shima gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawaya tabbatarwa da shugaban kasar da wannan barazana.

 

Saidai yace shugaban kasar ya gaya masa cewa, yayi taro da shuwagabannin tsaro kuma ya sanar dasu cewa su yi maganin ‘yan Bindigar.

 

Gwamman a rahoton Daily Trust ya kuma kara da cewa, shi dama ya dade yana kiran a dauki matakin yiwa dazukan da ‘yan Bindigar dake ciki ruwan bama-bamai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.