fbpx
Monday, August 15
Shadow

Buhari da gwamnonin APC sun so suyi magudi a zaben gwamnan jihar Osun

An zargi gwamnatin shugana Muhammadu Buhari cewa sun so suyi magudi a zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar jiya.

Deji Adeyanju dake kare hakkin bil’adama ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

Inda yace shugaban kasar da gwamnoninsa sun so suyi magudi a zaben amma sun kasa haka nan suka hakura aka ba PDP.

Kuma ya jinjinawa al’ummar jihar da suka tsaya suka jajirce aka kirga kuru’un a gabansu, sannan yace dole a kula don APC ba zatayi zaben adalci ba a watan febrairu mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.