fbpx
Saturday, August 8
Shadow

Buhari damfarar ‘yan Najeriya kawai yake>>A’isha Yusuf

‘Yar Rajin kare hakkin bil’adama da ta shiga gaba-gaba wajan fafutukar ganin an sako ‘yan matan Chibok,  Aisha Yusuf ta bayyana cewa shugaba Buhari da mutuminnan da aka kama dan najeriya a Dubai me damfarar Mutane ta yanar Gizo, Raymond Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppy duk halin su daya.

 

A’isha Ta bayyana cewa shugaba Buhari damfarar ‘yan Najeriya kawai yake inda tace har yanzu ya kasa bayyanawa mutane yawan kudin yakin neman zaben da aka tara mai a shekarar 2015 da kuma kadarorinsa.

A’isha ta bayyana cewa, a yayin da Hushpuppy ke damfarar mutane ta hanyar kudi shi kuwa Buhari na damfarar mutane ta bangaren kudi da Siyasa ne kamar yanda ta bayyana a shafinta na twitter.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *