Mai magana da yawun kungiyar dattawan Arewa, Dr. Hakim Baba Ahmad ya nemi shugaba Buhari daya ritaya ya mikawa Osinbajo mulki.
Baba Ahmad ya bayyana hakan ne biyo bayan maganar da shugaban kasar yayi na cewa ya kosa ya sauka a mulki ya mikawa wanda yaci zabe.
Wanda hakan ne yasa tsohon sakataren hukumar zaben ta INEC ya nemi shugaban kasar kawai yayi ritaya, domin abubuwa kara tabarbarewa kawai zasu yi.
A jiya itama kungiyar kare hakkin bil’adama ta HURIWA ta shawarci shugaban kasar daya yi ritaya tunda yace mulki akwai wahala kuma ya kosa ya sauka.