Tsohon shugaban Najeriya, Janar Yakubu Gowon ya bukaci ‘yan Najeriya Kiristoci su saka shugaban kasa, Muhammadu Buhari a addu’a, ya bayyana cewa shugaban na bukatar addu’a saboda kada Najeriya ta ruguje a hannunshi.
Gowon ya bayana hakane ta bakin Ministan ayyuka na musamman, George Akume wanda ya wakilceshi wajan nada sabon sakataren hukumar aikin Ibadar Kiristoci.
Yace yasan shugaban kasa, Muhammadu Buhari na iya bakin kokarinsa amma har yanzu akwai matsaloli a kasarnan, yace amma ta hanyar yin addu’a, za’a shawo kan matsalar.