fbpx
Saturday, June 25
Shadow

Buhari na son gamawa dani>>Tinunu ya koka

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa duk da ya taimakawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari wajan zama shugaban kasa amma yanzu shugaban kasar ya juya masa baya.

 

Bola Tinubu ya gayawa jama’ar sa na yankin jihohin Yarbawa ne haka inda yace kada su bari Buhari ya kunyatashi a idon Duniya.

 

Tinubu yace har a TV kowa ya gani shugaba Buhari sai da yayi kuka yace kuma ba zai sake neman takarar shugabancin Najeriya ba amma shine ya je ya karfafa masa gwiwa.

Karanta wannan  Tuna Baya: Kalli bideyon lokacin da Tinubu ya biyawa gabadaya daliban jihar Legas kudin jarabawar fita daga sakandiri ta SSCE

 

Tinubu yace bai taba rokon shugaban kasa, Muhammadu Buhari komai ba dan haka babu abinda yake nema a wajansa kawai dai a kare muradin yarbawa.

 

Yace kuma idan an yadda su za’a baiwa takarar shugabancin Najeriya to shi ya kamata ya zama shugaban kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.