fbpx
Monday, August 8
Shadow

Buhari Ya Baiwa Ministocinsa Mako 1 Don Kawo Rahotanni kan ganawar da suka yi da jama’a kan zanga-zangar SARS

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa dukkan ministocin shi mako guda domin su gabatar da rahotannin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihohinsu daban-daban kan rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar #EndSARS a fadin kasar.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake magana a shirin gidan Talabijin na Channels, ‘Sunrise Daily’.
Adesina ya ce shugaban ya ba da umarnin gabatar da rahotanni yadda ya kamata ga Sakataren Gwamnatin Tarayya a cikin mako guda, biyo bayan ganowar Buhari cewa ministoci biyu ne kawai suka shirya rahotonninsu har zuwa taron FEC na wannan makon.
Umurnin ya biyo bayan rikicin da ya biyo bayan harbe-harben da ake zargi na masu zanga-zangar #ndSARS a kofar Lekki da ke Legas.
Amnesty International da sauran masu rajin kare hakin dan adam sun yi zargin cewa sojoji da ‘yan sanda sun kashe a kalla mutane 12 a wurare biyu a Legas bayan harbin Lekki.
Sojojin Najeriya sun yi watsi da rahotannin a matsayin “labaran karya.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Yadda mutane kusan miliyan guda suka mamaye jihar Nasarawa domin nuna goyon bayansu ga Peter Obi

Leave a Reply

Your email address will not be published.