Shugaban kasar Najeriya Mejo Janar Muhammadu Buhari ya cewa Kashim Shettima sune zasuyi nasarar lashe zabe tare da maigidansa Tinubu a shekarar 2023.
Muhammadu Buhari ya bayyana masa hakane ne bayan Shettima ya kai masa ziyara jiya bayan an kaddamar dashi a matsayin abokin takarar Tinubu.
Hadimin shugaban kasar Najeriya, Garba Shehu ya wallafa wannan labarin.
A jiya dan takarar shugaban kasa na APC Tinubu ya kaddamar da Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.