fbpx
Monday, December 5
Shadow

Buhari ya cika korafi, Nine zan iya magance matsalar tsaro>>Wike

Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya bayyana cewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya cika korafi akan matsalar tsaro kuma alamu sun nuna cewa ya gaza.

 

Yace ta yaya matsalar tsaro ta hana mutane zuwa gonakinsu amma kana ce musu su koma gona?

 

Ya bayyana hakane a yayin ganawa da wakilan PDP a jihar Borno, Wike yace shine ya fi dacewa ya wakilci jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

 

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN yace Wike ya bayyana cewa yana da yakinin PDP ce zata lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2023.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *