fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Buhari ya gama amfani da Magu ne kawai yake son yadashi, kuma ku jira ku gani babu wani abu da zai faru kan binciken da ake masa duk bulace>>Buba Galadima

Tsohon na hannun damar shugaban kasa, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa Binciken Magu da shugaba Buhari ke yi ba da gaske bane. Yace ana yi ne kawai dan yaudarar ‘yan Najeriya a nuna musu cewa wai ana yaki da cin hanci.

 

Ya bayyana hakane yayin hira da Sunnews inda yace shugaban kasar ya kammala aiki da Magune yana son cireshi. Yace idan ba’a yi hankali ba akwai wasu na hannun damar Buharin da zasu so kawar da Magu.

Yace idan dai da gaske Binciken gaskiya akewa Magu to yana kalubalantar gwamnatin data yi binciken nashi a fili gaban ‘yan Jaridu. Yace amma ba zasu yi ba saboda idan aka yi haka, Asirai da yawa zasu tonu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.