fbpx
Monday, August 8
Shadow

Buhari Ya Gaza A Fannin Tsaro>>Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa

Biyo bayan yawaitar kashe-kashen dake ci gaba da wakana a jihohin Arewacin kasar nan da suka hada da Borno, Kaduna, Katsina, Sokoto, Taraba da sauran su hakan ya sa gammayar kungiyoyin matasan Arewa (CNG) ta nuna gazawar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ta gagara kawo karshen jinin wadanda ba su ji ba ba su gani ba da ‘yan ta’adda suke zubar wa ba dare ba rana.

 

 

A takardar dake dauke da sa hannun kakakin kungiyar, Abdul-Azeez Suleiman, Kungiyar ta kuma nuna takaicinta kan yadda ake neman siyasantar da kashe-kashen, wanda hakan na daya daga cikin dalilan karuwar ta’addancin.

 

 

Haka kuma gwamnati duk yunkuri da gwamnati ta yi na ganin ta kawo karshen kashe-kashe, garkuwa da mutane, rikicin kabilanci da sauran su a karshe ba ta iya daukar matakan da suka dace.

 

 

Don haka ne kungiyar ta CNG ta kudiri aniyar gudanar da zanga-zangar lumana domin ganin gwamnati da sauran wadanda suke da alhakin dakile matsalar sun dauki matakin da ya dace.

 

Karanta wannan  Ka gaggauta ajiye mukamin shugaban kungiyar kamfe ta Tinubu da APC ta baka, shugaban kirista ya fadawa gwamna La Long

 

Za a gudanar da zanga-zangar ne a ranar Talata mai zuwa a jihar Katsina kasancewar ta jihar da ta fi fama da matsalar kashe-kashe a yanzu.

 

 

Sannan daga bisani za a fadada zanga-zangar a biranen sauran jihohin Arewa a ranar Asabar mai zuwa.

 

 

Saidai a dalilin bulluwar cutar corona, akwai sharrudan gudanar da zanga-zangar, inda kowa zai sanya takunkumin fuska. Sannan kuma za a gudanar da shi cikin tsari da bin dokoki. Haka kuma an bukaci jama’a su sanya koren ganye a ababen hawansu ko wuraren kasuwancin su domin nuna goyon bayan su ga zanga-zangar kan kashe al’ummar Arewa da ‘yan ta’dda suke yi.

 

 

Za a janye zanga-zangar ne bisa la’akari da irin martani ko matakin da gwamnati za ta dauka, kafin kungiyar ta san matakin da za ta dauka a gaba.

 

 

Masu zanga-zangar za su hadu ne a fadar Sarakunan Gargajiya ko majalisun jihohi domin samun damar mika koken su don kaiwa gaba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.