(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Sai dai kuma Garba Shehu ya yi zargin cewa kila wasu ‘yan siyasa ne suka tattaro wasu tsiraru aka ba su kudi don su yi wa Buhari Ihu.
Kuma a cewarsa gari kamar Maiduguri, ba za a rasa yawan mutum da ya kai miliyan hudu ba zuwa biyar ba kuma tun da mutum ba Allah ba ne ba zai iya gamsar da kowa da kowa ba.
Ya ce gwamnatin Buhari ta nuna za ta iya yaki da Boko Haram kuma shugaban ya yi alkawalin canza matakan yaki na magance abin da ya kira sabuwar matsalar da aka samu.
Gwamnatin Buhari dai ta dade tana ikirarin karya lagon kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin arewa maso gabas, amma kuma har yanzu mayakan kungiyar na ci gaba da yi wa mutanen yankin barazana.
Harin da aka kai Auno ya fusata mutanen Borno, inda da dama suka zargi jami’an tsaro da sakaci bayan sun rufe hanyar shiga Maiduguri da yammaci, dalilin da ya sa mayakan Boko Haram suka riske matafiya a cikin dare.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:
A shafin twitter zaku same mu a @hutudole
A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole