fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Buhari Ya Tallafawa Al’ummar Da ‘Yan Bindiga Suke Kaiwa Hari A Jihar Katsina Da Tirela 139 Na Kayan Abinci

Gwamnatin Tarayya, karkashin ministan Jin Kai, Hajia Sa’adiya Faruk, ta damka Tirela dari da talatin da tara, domin tallafawa wadanda harin yan bindiga ya rutsa da su a kananan hukumomin Dutsinma da Batsari da Danmusa da Safana da Faskari da Batagarawa da Kankara da kuma Sabuwa. Domin rage masu radadin halin da yan bindigar suka jefa su.

 

 

Ministan ta bayyana hakan ne lokacin da ta kawo ziyarar jajantawa al’ummar jihar Katsina da kuma kawo masu tallafin kayan masarufi, wadda ta samu tarba daga Mataimakin Gwamna, Alhaji Mannir Yakubu.

 

Sa’adiya Faruk ta ce akwai masara kimanin tirela sittin da biyar da dawa tirela sittin da ukku da Kuma gero tirela 10. Haka Kuma akwai man girki da shinkafa da wake da gari da katifar kwanciya da tabarma da barguna rufa da ragar gidan sauro da bokitai da kuma gishiri. Za a rabawa magidanta dubu takwas da dari ukku da talatin da tara, wato Yan gudun hijira da suke kananan hukumomi takwas da matsalar tsaro ta addabe su.

Karanta wannan  Tekun Legas ya tafi da dalibai hudu da suka je murna bayan sun lashe jarabawar WAEC

 

 

Ministan Jin Kai ta kara da cewa wannan tallafi ya biyo bayan kudirin da Sanata mai Wakiltar Yanki Katsina ta Tsakiya ya gabatar a zauren majalisar Dattawa, Kuma ya samu karbuwa. Wanda ya zo ofis dina ya fi a kirga, domin ganin an kawo wannan tallafi a jihar Katsina.

 

 

Shima da yake jawabinsa, Mataimakin Gwamna, Alhaji Mannir Yakubu ya bayyana godiyarsa ga wannan tallafi da gwamnatin Tarayya ta kawo. Kuma ya sha alwashin ganin an raba su ga mabukata, musamman ga yan gudun hijira da suke wadannan kananan hukumomi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.