fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Buhari ya tattauna da Super Eagles ta bidiyo

Gabannin karawar da Ƙungiyar Super Eagles ta Najeriya za ta yi da Tunisia a yau a Kamaru a gasar cin kofin Afrika, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tattaunawa ta bidiyo da ƴan wasan na Super Eagles.

A wani saƙo da Shugaban ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya buƙaci ƴan wasan da su ci gaba da sa ƴan Najeriya farin ciki inda ya ce kada su tsaya a cin wannan wasa na yau kaɗai, su ɗauki kofin baki ɗaya.

Shugaban ya yi magana da kocin Najeriya Augustine Eguavoen da Keftin ɗin ƙungiyar Ahmed Musa da Amaju Pinnick wanda shi ne Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya da jakadan Najeriya a Kamaru Janar Abayomi Olanishakin mai ritaya.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: La Liga ta kai karan PSG wurin hukumar wasan kwallon kafa ta UEFA bayan Mbappe ya fasa komawa Madrid

Shugaban ya gode wa kocin Najeriya da sauran muƙarrabansa kan irin jajircewar da suke yi wajen ganin an samu nasara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.