fbpx
Friday, February 26
Shadow

Buhari ya taya Ngozi murnar zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Ngozi Okonjo Iweala murnar zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya, World Trade Organisation (WTO).

A yau Litinin ne aka tabbatar da tsohuwar ministar kuɗin ta Najeriya a matsayin mace kuma ‘yar Afirka ta farko da za ta jagoranci ƙungiyar bayan kusan wata shida ana ja-in-in-ja.

“A madadin Gwamnatin Tarayya da dukkanin ‘yan Najeriya, Buhari na taya tsohuwar ministar kuɗi, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, murnar zaɓenta a matsayin shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya,” a cewar sanarwar da Garba Shehu mai magana da yawunsa ya fitar.

Buhari ya ce ta jawo wa Najeriya “kwarjini da girmamwa”, yana mai cewa ta aiwatar da sauye-sauye masu yawa lokacin da take ministar kuɗi da kuma ministar harkokin waje.

Ngozi ta samu shugabancin ne bisa samun goyon bayan gwamnatin Amurka ƙarƙashin shugabancin Joe Biden kasancewar Donald Trump bai goyi bayanta ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *