fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Buhari ya tura tawaga ta musamman zuwa Sokoto da Katsina

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika da tawaga ta musamman zuwa Sokoto da Katsina sakamakon yadda ƴan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a yankunan jihohin.

Mai magana da yawun shugaban Najeriyar Malam Garba Shehu ya sanar da hakan inda ya ce shugaban yana jiran rahoto cikin gaggawa da kuma shawarwari kan matakin da ya kamata a ɗauka domin magance matsalolin da jihohin ke fuskanta.

Cikin waɗanda Buharin ya tura akwai babban mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da Babban Sufeton ƴan sandan Najeriya Usman Alkali Baba da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya Yusuf Magaji Bichi da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya Yusuf Magaji Bichi da kuma shugaban tsaro na rundunar sojin Najeriya Manjo Janar Samuel Adebayo.

Karanta wannan  Majalissar dinkin duniya tace harkar Crypto zata iya rusa Najeriya da sauran kasashen da suka cigaba

Wannan matakin dai na zuwa ne jim kaɗan bayan yan ƙasar da dama sun nuna ɓacin ransu kan kasashe-kashen da ake ƙara samu da garkuwa da mutane a ƙasar.

Ko a yau ma sai da wasu yan ƙasar suka fita zanga-zanga a wasu sassa na Najeriya har da Abuja babban birnin ƙasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.