fbpx
Saturday, June 25
Shadow

Buhari yace ya hakura da siyasa, ni naje na karfafa masa gwiwa ya fito takarar shugaban kasa a 2015>>Tinubu

Dan takarar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, shine ya je ya karfafawa shugaba Buhari ya sake tsayawa takarar shugaban kasa.

 

Yace bayan da shugaba Buharin ya tsaya takara har sau 3 bai yi nasara ba, ya nuna alamar gayija inda ya ce ba zai sake fitowa takarar shugaban kasa ba.

Tinubu yace shine ya tashi yaje har Katsina ya samu shugaba Buhari ya karfafa masa gwiwa kuma ya taimakeshi yayi nasara.

 

Tinubu ya bayyana hakane a Abeokuta yayin wata ziyara da ya kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.