fbpx
Friday, March 31
Shadow

Buhari zai shilla Chadi bikin rantsar da Mahamat Idriss Deby

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi Chadi a yau Litinin don halartar rantsar da Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta Jamhuriyar Chadi na tsawon shekara biyu.

Za a yi bikin rantsuwar ne a N’Djamena, babban birnin ƙasar, inda za a tattauna kan batun mayar da ƙasar turbar dimokradiyya, bayan mutuwar tsohon shugaban Idriss Deby Itno.

Mahamat Idriss Deby Itno, wanda aka kuma sani da Mahamat Kaka, ɗa ne ga marigayi shugaban Chadin Idris Deby.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Garba Shehu, mai taimaka wa Buhari kan yaɗa labarai, ta ce shugaban Najeriyar zai koma ƙasarsa bayan kammala rantsarwar

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *