fbpx
Thursday, December 7
Shadow

Buhari zai tafi Nijar taron ƙolin ƙasashen Afirka

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi Jamhuriyar Nijar domin halartar taron ƙolin ƙasashen Afika da kuma ƙaddamar da littafi.

A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan kafofin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar ya ce shugaban Buhari zai bar ƙasar ranar Alhamis domin halartar taron ƙoli na ƙasashen Afirka kan bunƙasa masana’antu da tattalin arziki.

Gabanin fara taron ƙolin shugaba Buhari zai halarci taron ƙaddamar da littafin – da Farfesa John Paden na jami’ar George Mason da ke Amurka – mai taken Muhammdu Buhari: ‘The Challenges of Leadership in Nigeria’.

Karanta wannan  Shugaban kasa, Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima zasu kashw Naira Biliyan 15 wajan Tafiye-Tafiye a shekarar 2024

Haka kuma shugaban zai halarci taro na musamman kan yarjejeniyar kasuwanci maras shinge tsakanin ƙasashen Afirka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *