fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

BUK VC: Farfesa Abbas ya lashe zaben fidda gwani na Jami’ar Bayero

Farfesa Sagir Adamu Abas ne yai nasarar lashe zaban fidda gwani da aka gudanar a jami’ar Bayero domin jagorantar mukamin mataimakin shugaban Jami’ar.

An dai gudanar da zaben ne, inda Farfesa Sagir ya kayar da abokan takarar sa har mutum uku.

Farfesa Adamu ya samu kuri’u 1,026 inda abokin karawarsa Farfesa Adamu Idris Tanko ya samu kuri’u 416.

Sai dai bayan zaban fidda gwanin da a ka gudanar, rahotanni sun nuna cewa, kafin a ayyana wanda yai nasarar zama shugaban jami’ar sai kwamitin tantancewa yayi wani zama wanda sune keda al’hakin bayyana wanda yai nasarar.

Karanta wannan  Ba karamar dama na baka ka zama mataimakina ba kuma kar kayiwa kudu maso gabashin kasar nan asara, Kwankwaso ya fadawa Obi

Ana sa ran kwamitin tantancewa zai gudanar da zagayan karshe a ranar Asabar Mai zuwa.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.