Kocin Madrid, Carlo Ancelotti ya zamo koci na farko a duniyar kwallon kafa daya lashe kofin gasar zakarun Nahiyar turai sau hudu, bayan Madrid ta doke Liverpool daci 1-0.
Kocin yayi nasarar lashe kofin ne su daya a kungiyar a AC Milan sannan kuma sau uku a kungiyar Real Madrid. Kuma ya zamo koci na farko daya kai wasannin karshe na gasar sau biyar tarihi.
Bayan an tashi wasan Ancelotti ya bayyana cewa tabbas Madrid ta cancanci lashe kofin domin ta taka rawar gani a wannan kakar, duk da cewa a farkon kakar su dan sha gwagwarmaya.